fbpx
Wednesday, May 25
Shadow

An sake gano Dala Miliyan 23 da ake zargin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha da sacewa

Hukumar bincike ta kasar Ingila, Britain’s National Crime Agency ta bayyana cewa ta sake gano kudi har dala Miliyan 23 da ake zargin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha da sacewa.

 

Abacha ya mulki Najeriya daga shekarar 1993 har zuwa mutuwarsa a shekarar 1998.

 

Kungiyar dake saka ido kan yanda gwamnatocin Duniya ke gudanar da mulki me suna Transparency International ta bayyana cewa, Ana zargin Janar Sani Abacha da sace dala Biliyan 5.

 

Hukumar ta Britain’s National Crime Agency ta bayyana cewa suna kokarin ganin kasar Ingila ba ta zama mafakar barayi masu sace dukiyar gwamnati ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published.