fbpx
Thursday, August 18
Shadow

An saki me tsaron lafiyar A’isha Buhari da yayi harbi a fadar shugaban kasa

Rahotanni sun bayyana cewa an saki Usman Shugaba, me tsaron lafiyar A’isha Buhari da yayi harbi a fadar shugaban kasa, Muhammadu Buhari lokacin hatsaniya tsakanin hadimin shugaban kasar,Tunde Buhari da iyalanshi.

 

Hutudole ya samo daga Sahara Reporters cewa an saki Shugaba ne a jiya, Litinin. Hakanan Rahotan ya kara da cewa Shugaba yasan abubuwa da yawa akan masu ruwa da tsaki a harkar gwamnati dake kallon A’isha Buhari a matsayin wata matsala dake hanasu cimma burinsu.

Hakanan ya kara da cewa fadan bai kare ba dan kuwa A’isha Buhari ta cimma damarar daukar fansa kan wannan terere da aka mata a Duniya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.