(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Kwamishinan labarai na jihar Borno, Babakura Jato ne ya bayyanawa manema labarai haka inda yace an saki rukunin farko na tubabbun ‘yan Boko Haram din a karkashin tsohon gwamnan jihar, Kashim Shattima yayin da aka saki rukuno na biyu dana uku a karkashin gwamna Babagana Umara Zulum.
Ya bayyana cewa yawancin wadanda aka saka din ba wai ainahin ‘yan Boko Haram bane.
Yace akwai ‘yan uwan ‘yan Boko Haram din daga ciki akwai kuma wanda aka kama da zargin cewa ‘yan Boko Haram ne amma bayan bincike aka gane cewa basu da alaka da kungiyar.
Yace sauran sune ‘ya’yan ‘yan Boko Haram din da kuma wasu ‘yan Boko Haram din da suka tuba. Saidai yace ba zai bayyana yawansu ba saboda tsaro.
Da yake mayar da martani kan tambayar cewa ana samun wasu suna komawa kungiyar Boko Haram din bayan sakinsu. Jato yace wannan jita-jita ce kawai amma abinda dai sukan fuskanta a wasu lokutan shine wasu tubabbun mutanen gari basu yadda dasu, dan haka idan aka samu irin wannan matsala akan dawo da mutum a canja mai mazauni.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:
A shafin twitter zaku same mu a @hutudole
A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa
Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole