fbpx
Saturday, January 16
Shadow

An sallami dansanda me shekaru 30 daga aiki bayan yiwa Yarinya me shekaru 14 fyade

Hukumar ‘yansandan jihar Ebonyi sun sallami wani dansanda me kimanin shekaru 30 da yawa wata yarinya me shekaru 14 fyade.

Dansandan ya fuskanci kotun ‘yansanda kuma an yanke hukuncin korarsa daga aiki, kamar yanda shugaban kungiyar kare hakkin bil’adama ta NHRC a jihar, Okorie Christopher ya bayyana.

 

Ya bayyana cewa sun jinjinawa hukumar ‘yansandan kan yanda ba’ayi rufa-rufa ba kan lamarin.

 

Yace yanzu kuma zasu shiga kotu tare da korarren dansandan dan kwatowa yarinyar Hakkinta.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *