Friday, May 29
Shadow

An sallami me Coronavirus/COVID-19 duka da be warke ba a Asibitin Abuja, Asibiti ya fadi Dalili

Babban asibitin gwamnatin Abuja ya bayyana dalilin da yasa ya saki wani me jinyar Coronavirus/COVID-19 duk da cewa be warke ba.

 

Mataimakin me yada labarai na Asibitin, Mr. Tayo Haastrup ne ya bayyana haka a babban birnin tarayya, Abuja, Yau Juma’a.

Yace a yanzu babu wani me cutar Coronavirus/COVID-19 da suke aje dashi ba bisa son ransa ba, yace mutane 35 ne aka kai Asibitin suna fama da cutar Coronavirus/COVID-19 kuma an sallami guda 27 daga ciki.

 

Ya kara da cewa saidai akwai wani mara Lafiya da ya kwashe kwanaki 45 a Asibitin kuma yaki yadda a dubashi wanda kuma kwajin da ake ta mai ya nuna cewa yana dauke da cutar.

 

Duk da Haastrup be kira suna ba amma an yi amannar cewa matarnance data zo daga kasar Ingila zuwa jihar Benue, me shekaru 58 watau Susan Idoko-Okpe.

 

Yace kusan duk wanda suka sallama ana salmarsune bayan sati 3 da shigarsu Asibitin.

 

Yace NCDC ta fitar da sabuwar doka dake cewa idan mutum ya kai kwanaki 45 a killace kuma bai nuna wata alamar cutar a jikinsa ba amma kuma bai warke ba to za’a iya sallamarsa ya koma gida ya killace kansa, saidai daga Lokaci zuwa Lokaci zai rika zuwa ana masa gwaji.

 

Ya kara da cewa wannan daliline yasa suka sallami wancan duk da bai warke ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *