Sunday, June 7
Shadow

An sallamo mahaifiyar Ronaldo daga asibiti

Manema labarai na La Gazetta Sport sun tabbatar da cewa an sallamo mahaifiyar Cristiano Ronaldo, Dolores Aveiro daga asibiti bayan an kwantar da ita ranar talata uku ga watan maris.

Dolores ta sha wahala ciwon barin jiki wanda hakan ya bata ran dan wasan gaba na juventus kuma ya bar kasar Italia ya dawo kasar shi ta Portugal don ya zauna tare da mahaifiyar shi.
An sallami Dolores mai shekaru 65 ne a ranar juma’a kuma hakan ya faranta ran Ronaldo. Ronaldo yace zai cigaba da zama a Madeira saboda an daga gasar Serie A.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *