Masu bincike sun ce an samu ƙarin waɗanda suka kamu da ciwon suga daga shekara ta 1990.
Binciken ya nuna cewa an samu ƙarin daga kashi 7 zuwa kashi 14 na manya da suka kamu da ciwon.
Zuwa yanzu akwai mutane miliyan 800 da suka kamu da ɗaya daga cikin nau’ukan ciwon suga.
Masu binciken sun gano cewa cutar na haifar da yanke gaɓa da ciwon zuciya da ciwon ƙoda da rashin gani da kuma mutuwa.
Sun ƙara da cewa mutanen da suka fi kamuwa da cutar sun fito ne daga ƙasashe masu tasowa, inda samun magani ya ke da matuƙar wahala.
Waɗanda suka gudanar da binciken sun ƙara da cewa abinci marasa inganci ne sahun gaba cikin abubuwan da ke haifar da ciwon suga tsakanin manya.