Tun bayan kama da kuma fara binciken Babban Akanta janar na kasa, Ahmad Idris da ake matsa kan satar Biliyan 200, ya bayyana sunayen jami’an gwamnati wanda ke da hannu a wannan badakala.
Zuwa yanzu dai an kama tsohon gwamnan Zamfara, Abdulaziz Yari da ake zargin ya karbi Biliyan 20 a wajan akanta janar din.
Akwai kuma shugaban Finex Professional, Anthony Yaro da shima aka kama.
Akwai kuma sauran wasu jami’an gwamnati dake cikin gwamnatin shugaban kasa da dama da suma ake shirin kamasu kamar yanda jaridar Economic confidential ta bayyana.