fbpx
Thursday, July 7
Shadow

An samu karin mutum 684 wanda suka harbu da cutar coronavirus/covid-19 a Najeriya

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 684 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar.

Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar juma’a 26 ga watan Yunin shekara ta 2020.
Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da:
Lagos-259 Oyo-76 Katsina-69 Delta-66 Rivers-46 Ogun-23 Edo-22 Osun-22 Ebonyi-21 FCT-20 Kaduna-16 Ondo-10 Imo-9 Abia-9 Gombe-5 Plateau-4 Bauchi-4 Ekiti-2 Anambra-1.
Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 8,253 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 554 a fadin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.