An samu labari daga fadar shugaban kasa cewa Muhammadu Buhari da wasu mukarrabansa na yiwa Tinubu zagon kasa, suna goyon bayan Atiku.
Manema labarai na Sahara ne suka ruwaito wannan labarin inda suka ce shugaban kasa Muhammdu Buhari baya goyon bayan dan jam’iyyarsa wato Tinubu, yana so arewa ta cigaba da mulki sai yasa yake goyon bayan Atiku na PDP.
Kuma rahoton ya kara da cewa shugaban kasar ne ya cewa mai kudin Katsina Dahiru Mangala ya koma PDP domin ya marawa Atiku Abubakar baya.
A karshe rahoton ya kara da cewa shugaba Buhari har makudan kukade ya baiwa Atiku domin ya biya bashin da gwamnatin tarayya ke bin kamfanoninsa gabanin zaben fidda gwani na PDP a watan Mayu.