fbpx
Thursday, July 7
Shadow

An samu sabbin mutum 790 wanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya Jimulla 26,484

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 790 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar.

Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar laraba 1 ga watan Yuli na shekara ta 2020.
Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanada suka hada da:
Delta-166 Lagos-120 Enugu-66 FCT-65 Edo-60 Ogun-43 Kano-41 Kaduna-39 Ondo-33 Rivers-32 Bayelsa-29 Katsina-21 Imo-20 Kwara-18 Oyo-11 Abia-10 Benue-6 Gombe-4 Yobe-2 Bauchi-2 Kebbi-2.
Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 10,152 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 603 a fadin kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.