fbpx
Friday, July 1
Shadow

An samu tashin gobara a wata ma’ajiya dake fadar shugaban kasa

An rawaito cewa gobara ta tashi a ranar Alhamis a wata ma’ajiyar kayayyaki dake kusa da ginin majami’ar fadar shugaban kasa dake villa Abuja, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.

Hakan na kunshene ta cikin sanarwar da mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya sanar Malam Garba Shehu.

Ya bayyana cewa gobarar ta tashine a sakamakon wutar lantarki, an kuma yi nasarar kashe wutar batare da wani bata lokaci ba, tun kafin zuwan ma’aikatan kashe gobara.

Ya kuma kara da cewa babu wani wanda ya samu rauni a sakamakon tashin gobarar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.