fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An sanya dokar hana zirga-zirga Na tsawan sa’o’i 24 a jihar Filato

Gwamna Simon Lalong na jihar Filato ya sanya dokar hana fita na sa’o’i 24 a kananan hukumomin Jos ta Arewa da Jos ta Kudu, daga karfe 8 na daren ranar Talata.

Gwamnan ya bayar da umarnin ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a gidan gwamnati da ke Jos.

Haka zalika gwamnan ya gargadi masu kunnan kashi, tare da umartar Jami’an tsaro da su kama duk wanda su ka samu da karya doka A jihar.

A karshe yayi kira da masu zanga-zangar adawa da rundunar SARS da su bi ka’idoji domin tabbatar da cimma burin muradan su, ta hanyar tattaunawa da gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published.