Masu hannun jari a kamfanunuwan jiragen Najeriya sun fara kokawa kan wahalar man jirgi a kasar wanda hakan yasa yawancin kamfanunuwan basa aiki.
Inda Benard, wani mai hannun jari a kamfanin jirgin sama ya bayyana cewa cikin kamfanunuwa 22 dake Najeriya guda hudu kadai ke aiki saruran 18 kuma an barsu haka nan.
Saboda haka yana baiwa gwamantin jiha dama tarayya bakidaya cewa su gina manyan shaguna a kamfamonin domin a cigaba da samun kudin shiga.