Tauraron dan wasan Bayern Munich, Robert Lewandowski ya shirya barin kungiyar tasa a wannan kakar yayin da shekara daya ce ta rage masa a kwantirakin shi.
Kuma manyan kungiyoyin nahiyar turai na harin sayensa kamar su Barcelona, PSG da Real Madrid, amma shi yafi son komawa Barcelona.
Inda tsohon tauraron dan wasan daya lashe kofin Firimiya, Chris Sutton ya bashi shawara cewa idan har zai koma Ingila to gara ya zabi Arsenal akan Manchester United.