Kungiyar masoyan Peter Obi ta bukaci dan takarar shugaban kasar na jam’iyyar Labour Party cewa ya fasa yin maja da jam’iyyar Kwankwaso ta NNPP.
Kungiyar sun bukaci ayi hakan ne bayan da suka fahimci cewa Rabi’u Kwankwaso ba zai taba janyewa Obi ba.
Mai magan da yawun kungiyar masoyan, Onwuasoanya Jones ne ya bayyan hakan cewa Obi ya gaggauta daina tattaunwa akan yin maja da NNPP.