fbpx
Thursday, June 8
Shadow

An shiga halin hau’lai a Jamus saboda karancin kwalaben giya

Kamfanonin giya sun yi gargadin cewa za a yi wahalar kwalaben giya a lokacin bazara saboda tsadar kayayyaki da ƙarancin motocin dakon kaya.

Lamarin ‘zai yi muni,’ kamar yadda shugaban kungiyar kamfanonin giya ya shaida wa jardar Bild ta Jamus.

Karancin kwalaben zai fi shafar ƙanana da matsakaitan kamfanonin giya, kamar yadda masani ya bayyana.

Kamfanonin giya za su biya kashi 80 na kwalaben giya fiye da yadda suka biya a bara. Giya ma za ta ƙara tsada.

Tsadar makamashi ne ɗaya daga cikin dalilin tsadar samar da kwalaben giya, kamar yadda kakakin wani kamfanin samar da kwalabe ya shaida wa jaridar Bild.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *