Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya yi Allah wadai da harin da ‘yan IPOB suka kai da ya kashe sojoji 5 a jihar Abia.
A baya dai, an yi tsammanin ba zai yi magana akan lamarin ba saidai yazo yayi maganar.
Amma kuma ya kaucewa kiran ‘yan IPOB din da ‘yan ta’adda.
Tsohon hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan inda ya dauko wani tsohon sakon na Peter Obi wanda yayi magana akan wani hari da aka kai jihar Filato inda ya kira maharan da sunan ‘yan ta’adda.
A zamanin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne dai aka ayyana kungiyar ta IPOB dake ikirarin kafa kasar Biafra da sunan kungiyar ta’ddanci.