Sunday, June 7
Shadow

An tabbatar da cewa Ronaldo da sauran yan wasan juventus basa dauke da cutar coronavirus

Juventus sun karbi sakamakon gwajin da aka yiwa yan wasan su wanda hakan yake tabbatar da cewa sauran yan wasan su basa dauke da cutar Covid-19.

 

Ranar 11 ga watan maris ne aka tabbatar da cewa dan wasan baya na Italia na dauke da cutar coronavirus daga baya kuma an samu wasu abokan aikin shi har guda biyu da cutar, sun hada da Dybala da Matuidi.
An samu budurwar Dybala Oriana Sabatini dauke da cutar coronavirus kuma hakan ya firgita matar Rugani Michela Persico wadda take dauke da ciki na tsawon watanni hudu.
Duk da cewa an tabbatar sauran yan wasan juventus basa dauke da cutar Covid-19, zasu cigaba da killace kansu har izuwa 25 ga watan maris don su cika makonni biyun da aka sa masu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *