Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour party, Peter Obi ya gana da gwamnan jihar Rivers Nyesom Wike a sirrince.
Peter Obi ya ziyarci Wike ne bayan daya dawo daga kasar Misra kwanan nan kuma bai bayyana abunda ya tattauna da Wike ba.
Amma dai a kwanakin nan ana rade raden cewa Wike na shirin sauya sheka saboda dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yaki zabarsa a matsayin abokin takararsa na zaben shekarar 2023.

