Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodu ya bayyana cewa ya tsawaita dokar kulle a jihar biyo baya alkaluman da suka gani na cutar.
A sanarwar daya fitar ta bakin me magana da yawunsa, Kunle Somorin, gwamnan ya bayyana cewa daya daga cikin kananan hukumominsu dake kan iyakarsu da wasu jihohi na daya daga cikin wanda gwamnatin tarayya ta bayyana a matsayin mafiya yawan masu kamuwa da cutar.
Yace dan hakane ba zasu bari abin ya zo ya fi karfinsu ba. Yace sun tsawaita dokar da kwanaki 14 kuma lokaci zuwa lokaci zasu ci gaba da duba yanda lamura ke gudana dan daukar sabbin matakai.