fbpx
Friday, August 12
Shadow

An wata ga wata: ‘Yan bindiga sunyi garkuwa da ‘yan sandan Najeriya guda goma

Labarin da muke samu yanzu na cewa ‘yan bindiga sunyi garkuwa da ‘yan sandan Nasarawa guda goma a jihar Kogi.

‘Yan sandan suna hanyar komawarsu Nasarawa ne ‘yan bindigar suka yi garkuwa dasu bayan sun hallaci zaben jihar Osun ranar 17 ga watan Yuli.

Motar jami’an ta samu matsala ne wanda hakan yasa ‘yan uwansu sukayi gaba suka barsu, su kuma ‘yan bindigar suka bullo daga daji suka yi wuff dasu suka tsere.

Amma hukuma ta zuba jami’ai sosai a yankin domin a kama ‘yan bindigar kuma a ceto jami’an da sukayi garkuwa dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.