Wasu magoya bayan Tinubu a farfajiyar zaben fidda gwani na APC dake Abuja sun sha barkonon tsohuwa.
Magoya bayan sun je da niyyar shuga wajan taron amma ‘yansanda suka hanasu, abinda ya kawo tashin hankalin kenan da ya kai ga aka watsa musu barkonon tsohuwa.
Taron zaben fidda gwanin na APC dai na cike da rikici wanda ake yi tsakanin musamman ‘ya takarar jam’iyyar dake neman tikitin takarar shugaban kasar.