Tauraron mawamin Hausa, Ali Isa Jita ya yi tambayar cewa shin wai ina shugaban kasa, Muhammadu Buhari yake?
Yace an yi kashe-kashen mutane irin wannan amma wai sai wani Wakili ne yake gayawa ‘yan kasa ga abinda shugaban kasa ya fada. A cikin Wani Bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Sada zumunta, Ali Jita ya bayyana cewa, a baya, kamin ya hau mulki, shine da irin wannan abu ya faru yake fitowa ya fara magana, yana nuna son talakawa.
Yace amma yanzu yayi Shiru. Yace abu daya ne ya fito Zahiri, Shuwagabannin da muke dasu yanzu sun gaza. Jita yace abinda ya kamata shine Matasa su tashi tsaye su nemarwa kansu Mafita.
https://www.instagram.com/tv/CIQrgUPAiqu/?igshid=18lfxorljqd2c