fbpx
Saturday, May 21
Shadow

An yanke wa limamin masallaci shekaru 5 a gidan yari sakamakon kashe alade a Rwanda

An yanke wa limamin masallaci shekaeu 5 a gidan yari sakamakon kashe alade a Rwanda.

Wata kotu a Rwanda ta ɗaure wani malamin addinin Islama har na tsawon shekara biyar a kurkuku sabo da ya kashe wani alade a harabar wani masallaci.

Wasu shaidu uku sun shaida wa kotun cewa sun ga limamin mai suna Sadate Musengimana yana dukan aladen da wani katako matakin da ya kashe shi nan take.

Sai dai lauyansa ya shaida wa kotun cewa ba da gangar ya kashe aladen ba, yana cewa ya yi kokarin koran shi daga harabar wani masallaci da ke gundumar Kayonzo a gabashin kasar ne cikin watan Fabrairu.

Karanta wannan  Hotuna Da Duminsu: Sojojin Najeriya sun kama tulin makaman 'yan IPOB

“Da yaji yara na cewa wani alade ya shiga masallacin, sai ya fito da wata sanda domin ya kore shi. Ya daki aladen kuma ya mutu, amma bai yi niyyar kashe shi ba,” kamar yadda lauyansa Yusuf Nsengiyumva ya shaida wa BBC.

Lauyan ya ce ya daukaka kara kan wannan hukuncin “mai tsanani”.

Tun watan Fabrairu ake tsare da Liman Musengimana, watan da ya kashe aladen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.