fbpx
Monday, March 1
Shadow

An yanke wa wani mutum hukuncin bulala 12 saboda satar doya a Abuja

Wata kotun yanki da ke Zuba, Abuja, a ranar Juma’a, ta yanke wa wani, Hashirmu Babagida, hukuncin bulala 12 saboda satar doya da kudin ta ya kai N596,000 a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Babangida, mazaunin Dankogi Garage, Zuba, ‘yan sanda sun tuhume shi da laifin sata.
Mai Shari’a Gambi, wanda ya yanke hukuncin, ya gargadi wanda ake kara da ya guji aikata hakan.
Tun da farko, lauya mai shigar da kara, Mista Chinedu Ogada ya fada wa kotun cewa a ranar Disamba. 27, 2020 mai shigar da karar, Tanko John, ya kai rahoton lamarin ofishin ‘yan sanda na Zuba.
Ogada, ya fadawa kotun cewa a ranar Disamba. 26, Babangida ya kutsa kai cikin gonar John, wanda ke Zuba, Abuja, ya kuma saci doya wanda ya kai N596,000.
Ya ce yayin binciken da ‘yan sanda ke yi, Babangida ya amince da aikata laifin kuma an kwato doya da aka sata daga gare shi.
Mai gabatar da karar ya ce laifin ya ci karo da sashi na 287 na Penal Code.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *