fbpx
Friday, July 1
Shadow

An yankewa dan wasan Atletico Madrid, Diego Costa hukuncin watanni shida a gidan yari

An kama tsohon dan wasan Chelsea da laifin zamba cikin amince wurin biyan kudin haraji kuma an yanke mai hukuncin watanni shida a gidan yari, Amma yanzu dan wasan ba zai je gidan yarin ba yayin da zai biya kudin fansa na euros 485,324 a cewar masu shari’a na kasar Spain.

Costa ya yiwa kasar Spain zambar euros 900,000 bayan bai bayyana kudin daya biya ba na sama da euros miliyan hudu a lokacin daya koma Chelsea a shekara ta 2014, da kuma wata euros miliyan daya ta fannin hotuna.
A safiyar yau Costa yaje wata kotu a garin Madrid domin ya tabbatar da yarjejeniyar amma mai magana da yawun kungiyar Atletico ya bayyana cewa Costa ya riga da ya biya kudin fansar tun a kwanakin baya kuma an janye maganar kaishe kurkuku.
Diego Costa ya koma kungiyar Atletico Madrid a shekara 2017 kuma kwallaye guda biyu kadai yaci a wannan kakar wasan saboda yana fama da rauni.
Wasu daga cikin manyan yan wasan kwallon kafa kamar Ronaldo da Messi suma sun biya kudin fansa a shekarun da suka gabata duk dai akan matsalar harajin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Za'a ba wanda ya lashe gasar tseren Marathon dala 80,000 a jihar Abuja

Leave a Reply

Your email address will not be published.