fbpx
Friday, August 12
Shadow

An yankewa magidanci hukuncin rataya a jihar Jigawa bayan ya kashe matarsa

Babban kotun jihar Jigawa dake Dutse ta yankewa wani magidanci hukunci kisa ta fannin rayaya saboda ya kashe matarsa.

Shu’aibu Adamu dan shekara 28 ya kashe matarsa ne a ranar 24 ga watan Yuni shekarar 2022, wanda hakan yasa mai shari’a Ahmad Muhammad Abubakar ya yanke masa hukunci daidai da laifin nasa.

Alkali Ahmad ya bayyana cewa Shu’aibu Adamu ya sabawa doka sashe na 221 ne kuma an samu kwararen shaidu daga bakin mutane hudu.

Saboda haka ya yanke masa hukuncin kisa ta fannin rataya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.