Wani mutum, Allen Abel ya gamu da fushin Kuliya a jihar Borno inda aka sameshi da laifin yaudara akan shirya wani tsarin bada tallafi na karya.
Mutumin ya tara kayan Abinci na sama da Miliyan 12 da sunan zai bada tallafi ne a karkashin ma’aikatar kula da Ibtila’i da Jinkai.
Saidai da aka tabbatar da karya yace, kotu ya yanke masa hukuncin shekaru 125 a gidan yari.