Alkalin kotun majistare Ibrahim Emmanuel a ranar Alhamis ya umarci wata matar aure Hadiza Ahmed da ta share harabar kotun na tsawon kwanaki biyar saboda ta yi wa makwabcinta duka.
Mista Emmanuel, ya ba da umarnin ne biyo bayan amsa laifin da Misis Ahmed ta yi.
An umurce ta da tsaftace harabar kotun na tsawon kwanaki biyar a karkashin kulawar magatakardar kotun.
Alkalin ya kuma ce, hukuncin zai zama darasi ga mutanen da ba su son zama lafiya da makwabta.