Kotun shari’ar musulunci dake jihar Bachi ta yankewa wasu ‘yan luwadi 3 hukuncin kisa ta hanyar jifa.
Maishari’a, Munka’ilu Sabo Ningi me ya yanke hukuncin bayan kammala sauraren shaidu da masu gabatar da kara.
Hakanan kuma duka wadanda ake zargin sun amsa laifukansu.
Wadanda aka yankewa hukuncin sune Abdullahi Abubakar Beti (30); Kamilu Ya’u (20) da kuma Malam Haruna (70).