Hukumar da ke kula da makamashin gas ta Saudiyya ta sanar da ƙarin kuɗin gas ɗin girki da kashi 9.28 cikin 100.
Hakan na nufin sabon farashin gas ɗin zai kai riyal 18.85 bayan fitar da haraji.
Jaridar Saudi Gazette ta rawaito cewa sai dai babu kudin dakon man da kuma raba shi a gidajen mai a ciki.
A yanzu yan kasar za su rika cika matsakaiciyar tukunyar gas da karin kashi 8.7 a kan farashin gas din na da.