Fadar Shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka sa Majalisar Jihar ta amince da bukatar afuwar tsohon Gwamna Joshua Dariye na Jihar Filato da Jolly Nyame na Jihar Taraba.
A wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce an yafewa Dariye da Nyame ne saboda rashin lafiya da ke barazana ga rayuwarsu.
Idan za a tuna a makon da ya gabata ne Shugaba Buhari a taron Majalisar Dokokin kasar ya yi wa tsofaffin gwamnonin kasar nan guda biyu da aka daure a gidan yari bisa laifukan cin hanci da rashawa da suka aikata a lokacin da suke kan mulki afuwa. Biyo bayan korafe-korafen da jama’a suka yi na yin afuwa, a yanzu fadar shugaban kasar ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana dalilin da ya sa aka yiwa ‘yan siyasar afuwa.
Sanarwar ta gara da cewa; anyi masu afuwa kan Sashi na 175 (1) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999.