Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ta yi watsi da zaben duk wani alkalin wasa na Najeriya bayan ta zabi wasu jami’ai 8 daga wasu kasashen Afirka da za su yi alkalanci a gasar cin kofin duniya na bana a Qatar.
FIFA ta fitar da sunayen alkalan wasa takwas na Afirka a cikin alkalan wasa 36, mataimakan alkalan wasa 63 da kuma jami’an VAR 36 da za a zaba a gasar.
Hukumar kwallon kafa ta duniya za ta bayyana jerin sunayen alkalan wasa na karshe wata daya kafin a fara gasar cin kofin duniya.
Alkalan wasan Afrika da ke cikin jerin sun hada da;
Victor Gomez (Afirka ta Kudu)
Janny Sikazwe (Zambiya)
Jean Jacques Ndala (DRC)
Mustapha Ghorbal (Aljeriya)
Redouane Jiyed (Maroko)
Tesssema Balmak (Ethiopia)
Maguette N’diaye (Senegal)