fbpx
Monday, June 27
Shadow

An yi yunkurin kaiwa Jihar Kano harin da ba’a taba kai irinshi ba a Najeriya, saidai mun dakileshi>>Sojojin Najeriya

Jami’an tsaro sun daƙile wani yunƙurin kai hari a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, “wanda ka iya zama mafi muni” a ƙasar, a cewar Babban Hafsan Tsaro na Najeriya Janar Lucky Irabor.

Janar Irabor ya bayyana hakan ne a yau Lahadi yayin da ya bayyana cikin wani shiri kan Ranar Dimokuraɗiyya a kafar talabijin ta Channels TV.

Ya ce an daƙile harin ne a Kano cikin makon da aka kai hari kan wata coci a garin Owo na Jihar Ondo, wanda ‘yan bindiga suka buɗe wa masu ibada wuta tare da kashe mutum fiye da 40.

“Babu mamaki ba ku da labari cewa a makon da ya wuce kaɗai da aka kai harin coci a Owo, a Kano misali, mun yi nasarar daƙile harin da ka iya zama mafi muni a ƙasar nan tamu saboda bayanan sirri da muka samu,” in ji shi.

Karanta wannan  'Yan bindiga sun kashe manoma 11 a jihar Sokoto

“A wannan aikin, mun gano kayayyakin da ake haɗa abubuwan fashewa da su. Mun ƙwace ƙunshin makamai masu yawan gaske da miyagu ke ƙoƙarin yin amfani da su a sassan ƙasa, har da Abuja.”

Janar ɗin ya ƙara da cewa harin Owo da aka kai ba ya nuna cewa ba a samun ci gaba a faɗin Najeriya ba, yana mai cewa “harkokin tsaro sun inganta a shekara ɗaya da ta wuce”.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.