Wasu bata gari sun yiwa mata da yarinyarta ‘yar shekara shida fyade a kasar Indiya a cikin mota bayan sun dauke su da manufar rage masu hanya.
Mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa bata san adadin mazajen dake cikin motar ba, amma sun hau ne don ya taimaka masu ya kai su gida.
Amma daga bisani mutanen dake cikin motar sunyi mata fyade tare da yarinyar tata ‘yar shekara shida kafin suka jefar dasu a wurin.
Inda matar tayi kokarin kaisu kara wurin hukumar ‘yan sanda wadda ke bincike akan lamarin yanzu, kuma hukumar ta kaisu asibiti don duba lafiyarsu.