fbpx
Thursday, February 9
Shadow

An yiwa matar da ta zagi motocin shugaban kasar Amurka sha tara ta arziki

Rahotanni sun bayyana cewa matarnan ‘yar kasar Amurka da ta zaki jerin motocin shugaban kasar  lokacin da suka zo wucewa ta gefenta tana kan keke kuma sanadiyyar hakan aka koreta daga aiki, abin ya zamar mata gobarar titi a jos, domin kuwa bayan korar ta daga aiki ne sai wani, da abinda tayi ya birgeshi ya bude wani asusun taimaka mata, ai kuwa ashe da yawa daga cikin amurkawan na jiran irin wannan dama, aka yi ta zuba taimako a wannan asusun.

Yanzu haka dai kudin da aka tarawa matar sun kai dalar Amurka dubu dari kamar yanda kafar labarai ta CNBC  ta ruwaito, da yawa da suka baiwa wannan matar tallafin kudin sun bayyana cewa matar tayi abinda ya musu dadi.

Karanta wannan  A jihar Edo ma Zanga-zangar karancin Naira ta barke wadda harvta tilasta kulle bankin CBN na jihar

Itama dai matar ta godewa mutanen da suka bata taimakon wannan kudi kuma tayi alkwarin zata yi amfani dasu yanda ya kamata.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *