fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

An yiwa ‘yar shekaru 6 fyade da yasar da gawarta a Kaduna

Karamar yarinya ‘yar shekaru 6 da aka ga gawarta a unguwar Kurmin Mashi dake Karamar hukumar Kaduna ta Kudu ta tayarwa da mutane hankali.

 

Lamarin yasa Kwamishiniyar Walwala da jin kai, Hajiya Hafsat Baba ta nemi ‘yansanda su yi bincike akai dan gano wanda suka yi wannan aika-aika.

 

Hajiya Hafsa tace wannan ba shine karo na farko ba dan haka ya kamata a gano wanda suke wannan aiki kamin su kai ga yin wani.

 

Tace gwamnatin jihar ta saka doka dan maganin irin wadannan miyagu amma wannan abu da suke yi ba zai sa a yi kasa a gwiwa ba wajan hukunta duk wanda aka kama.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Saidai kakakin ‘yansandan jihar, Muhammad Jalige ya bayyana cewa, yayi wuri a ce fyadene akawa yarinyar.

 

Yace sun kai gawarta wajan Likitoci dan yin gwaji a gano ainahin abinda ya kashe ta. Yace bayan kammala gwajin za’a mikawa iyayenta gawar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.