An zabi Bashiru Muhammad dan asalin jihar Sokoto a matsayin shugaban kungiyar dalibai ‘yan Najeriya da ke zaune a Turai.
Dalibin da ke digirinsa na biyu a jami’ar Coventry ya lashe zaben da kuri’u 326 cikin 400 na duka kuri’un da aka kada a zaben da aka yi a Istanbul, Turkiyya.
Ya samu nasara ne kan abokan hamayayyarsa uku.
Tun bayan kafa kungiyar a 2001, wannan ne karon farko da aka zabi dan arewa ya jagoranci kungiyar.
Sabon shugaban zai jagorancin kungiyar da ke da mambobi miliyan uku na wa’adin shekara hudu.