fbpx
Saturday, September 23
Shadow

An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

Zarge-zarge sun yi yawa akan cewa, ana biyan malaman makaranta albashin da bai wuce Naira Dubu 6 ba a wasu kananan hukumomin jihar Borno.

 

An rika samun wasu ‘yan asalin jihar ta Borno na wallafa alert din albashin a matsayin shaida na cewa dubu 6 ake biyansu.

 

Hakanan binciken hutudole ya samu bayani daga bakin wasu ‘yan asalin jihar ta Borno inda suka ce wannan lamari ya dade yana faruwa.

 

A martaninsa, Gwamna Zulum yace tabbas ana biyan wasu malaman makarantar jihar Albashin da baikai Naira dubu 11 ba.

 

A martaninsa ta bakin kakakinsa, Malam Isa Gusau, Gwamna Zulum ya bayyana cewa suna da malaman makaranta 17, 229 a kananan hukumomin jihar.

 

Da ya samu rahoton cewa, ba’a biyansu kudaden albashin da ya kamata da ya kai mafi karancin albashin 30,000, sai ya sanya a yi bincike akansu dan gano cancantarsu.

Karanta wannan  Za a fara gwajin riga-kafin cutar HIV a Afirka ta Kudu

 

Yace abin tsoro shine malamai 11,790 daga cikinsu basu cancanta aiki ba, wasu basu da takardun makaranta, wasu basu da kwarewa da dai sauransu.

 

Yace wadanda aka samu suna da kwarewa an fara biyansu albashinsu, amma sauran maimakon a koresu aiki shine ake shawarar a mayar dasu wani bangaren aiki a jihar.

 

Gwamnan ya kara da cewa, duka malaman dake aiki a karkashin gwamnatin jihar na samun albashin da ya kai matakin mafi karanci na 30,00.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *