Wani babban limamin coci da aka sace kwanannan ya zargi cewa jami’an tsaron Sojojin Najeriya na taimakawa masu garkuwa da mutane wajan satar mutanen da suke.
Saidai hukumar sojojin tace wannan ikirari ne kawai wanda babu wani bincike ko madogara tsayayya da aka yi amfani da ita wajan tabbatar dashi.
Hukumar sojojin tace tana taka tsantsan wajan ganin aika jami’an ta aiki dan haka basa irin wancan abin da ake zarginsu da yi.
Hukumar tace kasancewar bata daukar rashin da’a da wasa zata tunkari wannan malamin coci da yayi wannan zargi dan ya bata hujjar zarginsa.