fbpx
Friday, January 15
Shadow

An zargi wasu makiyaya da yin garkuwa da mutane uku tare da neman fansar Naira miliyan N1.2 A Jihar Kogi

Wasu da ake zargin makiyaya ne sun yi garkuwa da wasu ma’aikatan kamfanin karafa na Ajaokuta Steel Company Limited (ASCL) a jihar Kogi.

An rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, a kusa da rukunin ma’aikatan kamfanin SAE, yayin da makiyayan suka yi wa wadanda su Kai garkuwa dasu kwantan bauna, dauke da muggan makamai suka kuma tilasta musu shiga daji, kamar yadda wasu mazaunan yankin suka shaida hakan.

Wata majiya daga dangin wadanda lamarin ya rutsa dasu sun shaida cewa masu garkuwan sun tuntubi iyalan wadanda abin ya shafa inda su ka nemi a ba su Naira miliyan 1.2 kudin fansa kafin su sake su.

A cewar wasu mazauna yankin sun bayyana cewa, Makiyayan sun kama a kalla mutane 4 amma sun saki mutum daya kasancewar bashi da lafiya kuma tsoho ne mai yawan shekaru.

Da aka tuntubi Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, William Aya ya shaida wa wakilin jaridar Tribune cewa har yanzu rundunar ba ta samu rohoton ba a hukumance, inda ya bada tabbacin cewa zai waiwaye manema labarai dazarar sun bincika rahoton.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *