Rundunar sojin Najeriya ta zuba dakarunta sosai a babban birnin tarayya biyo bayan harin da aka kaiwa gidan kurkuku na kuje a makon daya gabata.
Wanda a harin suka saki baragari da dama da aka kulle a cikin kurkukun kuma gwamnati ta bayar da hotuna da sunayen wasu bata garin da suka tsere sannan an fara kama su.
‘Ya ta’addan sun sha alwashin sake kai wani hari a babban birnin tarayyar kuma sunce sun kai hari gidan kurkuku ne don su dakko wasu membobinsu su yaki kiristoci.
Wanda hakan yasa aka zuba jami’ai sosai a babban birnin tarayyar don gujewa wannan harin da suka ce zasu sake kawowa.