fbpx
Thursday, August 11
Shadow

An zuba jami’an tsaro sosai a Maiduguri yayin da shugaba Buhari ke shirin kai ziyara

An zuba jami’an tsaro sosai a Birnin Maiduguri na jihar Borno yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke shirin kai ziyara garin.

 

Shugaba Buhari zai kaddamar da ayyukan da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya yi.

 

Kwamishinan ‘yansanda na jihar, Abdu Umar ya bayyana cewa, an saka jami’an tsaro sosai dan shirin zuwan shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

 

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN ya bayyana cewa, kwamishinan yayi kira ga mutanan Maiduguri su zama masu bin doka da oda.

Leave a Reply

Your email address will not be published.