Kungiyar kare muradun inyamurai ta Ohanaeze Indigbo ta bayyana cewa, ana baiwa Inyamuri shugabancin Najeriya, zai magance matsalar tsaron kasar.
Sakararen kungiyar, Mazi Okechukwu Isiguzoro ne ya bayyana haka a wata sanarwa da suka fitar kan harin da aka kai kan jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja.
Ya bayyana cewa, suna aika sakon ta’aziyya ga shugaban kasa da kuma al’umma kan harin wanda na siyasa ne.