A satin daya gabatane mukaji labarin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar ganduje ya baiwa masu shayi dubu biyar tallafi , wannan batu ya dauki hankulan mutane sosai a kasarnan ta yanda wasu suka yaba, wasu kuma suka kushe.
Wadanda ke kushe wannan yunkuri na gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje na ganin cewa wai wannan tallafi daya bayar wulakancine ga al’ummar jihar Kano, duk irin masu ilimi da masu sana’o’i dake akwai a Kano a rasa wadanda za’a baiwa tallafi sai masu shayi, wannan ai yarfine, a ganinsu.
To amma masu kare wanan muradi suna ganincewa da babu gara ba dadi kuma, a kullum bawai sai wanda yayi karatun boko bane kadai yake bukatar tallafi daga gwamnati, suma masu shayinnan ‘yan kasane, suna da iyali, idan Allah ya sanyawa wannan sana’a tasu albarka babu abinda bazasu yi da itaba.
Shinma matasa ‘yan kwalisa, musamman gwagware kai harma da masu auren nawane suke fakewa a teburan masu shayi da safe kamin su fita wajan aiki da kuma da yamma bayan sun dawo?
To sai ace baza’a tallafawa masu shayi ba? Kawai dan wasu na musu kallon cewa suna sana’ar kaskancice, kai gwamna Ganduje kayi abin yabo da wannan tallafi Allah ya baka ikon sauke nauyin dake kanka, inji su.
Gaskiya sana’ar shayi tana daya daga cikin kananan sana’o’i da suka tallafawa tattalin arzikin kasar Arewa, kai harma da wasu daga cikin jihohin kudu, matasa da basu da girman kai suna samun aikin yi, yan kasuwa,za’a sayi madara,siga, dadai sauransu, wannan duk hanyar habbaka tattalin arzikice.
A kasashen da sukaci gaba harkar shayi tana da matsayi.