Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Kabir Gombe yayi karin haske kan dalilin da yasa basawa shugaba Buhari irin caccakar da sukawa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Ya bayyana hakane a wani bidiyo da ya watsu sosai a shafukan sada zumunta.
Malamin yace, dalili shine shi shugaba Buhari ya basu dama su rika zuwa suna gaya mai gaskiya wanda a lokacin Jonathan basu damu wannan damar ba.
Ya kara da cewa, idan shugaba ya bayar da damar a rika mada nasiha a biyr, haramun ne a hau mumbari a caccakeshi amma idan kuma bai bayar da wannan dama ba to dolene a caccakeshi akan mumbari.