Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, ya bayar da karin haske kan ma’aikatar wutar lantarki ta kasa da ta ruguje a ranar Juma’a, 8 ga Afrilu.
A cikin sanarwar da ya fitar a shafinsa na Twitter a yammacin yau, Abubakar ya ce masu kula da na’urorin suna kan aiki tukura. Ya kuma bayyana cewa wutar ta lalace ne sakamakon ayyukan wasu bata gari da suka lalata wasu na’urorin samar da wutar lantarki.