Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa, wasu bata gari na shirin kai hari Babban birnin tarayya, Abuja a yayin bukukuwan karshen shekara.
Saidai tuni hukumar kula da shige da fici ta NIS ta saka jami’anta a iyakokin Najeriya daban-daban dan tarar matsalar.
NIS tace ta samu daga fadar shugaban kasa cewa, ‘yan ta’adda daga Mali na shirin shigowa ta Nijar dan kawo hari a Abuja.
Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro dan ganin ‘yan ta’addar basu cimma burinsu ba.