Wednesday, January 22
Shadow

Ana fama da tsananin zafi a Saudiyya yayin da ake shirye-shiryen fara aikin hajji

Yayin da ake shirye-shiryen soma aikin hajji gadan-gadan a ƙasar Saudiyya, ana nuna damuwa kan yadda yanayin zafi ke ƙaruwa a birnin Makka da kewaye inda ake gudanar da ibadar ta hajji.

Hakan na zuwa ne yayin da dubun dubatar Musulmi ke ci gaba da kwarara zuwa birnin mai tsarki gabanin somawar aikace-aikacen hajji a ranar Jumu’a.

Hukumomin ƙasar kan yi tanadin na’urorin da za su taimaka wa maniyyata wajen rage zafin da suke fuskanta.

Fiye da mutum miliyan 1.3 ne za su gabatar da aikin hajji a wannan shekara

Karanta Wannan  Hotunan Mahajjata da aka kama sun yi safarar Kwa-ya zuwa kasa me tsarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *